Rikici yaki-ci-yaki-cinyewa a tsakanin gwamnatin kasar Afrika ta tsakiya da dakarun da ke adawa da gwamnatin har tsawon sama da wata guda, kuma a karkashin shiga tsakani da kungiyar AU da kungiyar raya tattalin arziki na kasashen yankunan tsakiyar Afrika da kasashen da abin ya shafa suka yi, a ranar 11 ga wata, bangarorin da rikicin Afrika ta tsakiya ya shafa sun daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta cikin wata sanarwa, kana da yarjejeniyoyin siyasa tsakaninsu.
Hong Lei ya ce, kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su dauki hakikanin mataki don aiwatar da yarjejeniyar da aka daddale tsakaninsu, don sa kasar ga alkiblar samun bunkasuwa yadda ya kamata, kuma kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen duniya, don ci gaba da taimakawa Afrika ta tsakiya wajen cimma dauwamammen zaman lafiya da na karko. (Bako)