Rahotanni sun ruwaito bangaren soji na Afrika ta tsakiya na cewa, a ranar 28 ga wata, wasu jiragen saman yaki sun yi jigilar sojoji da makamai daga kasar Gabon zuwa birnin Bangui. Ban da wannan kuma, motocin sojojin Faransa dake sintiri da motoci masu sulke sun tashi daga kasar Kamaru don shiga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
A ranar 27 ga wata, shugaban kasar Faransa François Hollande ya fada wa kafofin yada labaru cewa, kasashen duniya ba za su amince yanayin jin kai da ake ciki a jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya ci gaba da tabarbarewa ba, kuma hakkin Afrika ta tsakiya ne ta sauke nauyin da ke wuyansa game da halin da ake ciki a kasar.
Kwanan baya, dakarun Seleka gabilin su Musulmai da wasu dakarun tsaron kai na kananan hukumomin kasar galibinsu kiristoci sun yi artabu a tsakaninsu, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 100, tare da haddasa tabarbarewar al'amura.(Bako)