Wani mutum da ke da alaka da manyan jami'an soji da ke birnin Bangui hedkwatar Afrika ta tsakiya ya bayyana cewa, a ranar 7 ga wata, rundunar sojoji masu tsaro kai ta kananan hukumomin kasar sun fara kai farmaki ga wani kauyen da ke yankin arewa maso yammacin kasar, kuma abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3, tare da jikkatar wasu sama da 10, daga bisani kuma, kawacen dakarun Seleka sun fatatake su. Ya zuwa ranar 8 ga wata da safe, ana ci gaba da rikici a tsakaninsu, kuma abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 50. haka kuma, mazaunan kauyen sun riga sun bar kauyensu, kuma sun buya a gandun daji.
Kwanan nan, dakarun Seleka da ke bin addinin musulunci da rundunar sojojin tsaron kai ta kananan hukumomin kasar masu bin addinin kirista sun kara yin rikici mai tsanani a tsakaninsu.(Bako)