in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tube firaministan Afirka ta Tsakiya daga mukaminsa
2013-01-13 16:42:39 cri
Ranar Asabar 12 ga wata, gidan rediyon kasar Afirka ta Tsakiya ya watsa umurnin da Francois Bozize, shugaban kasar ya sa hannu a kai, inda aka sanar da tube firaministan kasar Faustin-Archange Touadera daga mukaminsa.

Matakin da mista Bozize ya dauka yana cikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatinsa da kawancen dakarun masu adawa da gwamnatin suka daddale a birnin Libreville, hedkwatar kasar Gabon a ranar 11 ga wata. Bisa tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar, an ce, bangarorin 2 sun amince da kafa gwamnatin hadin gwiwa, tare da gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a cikin shekara daya mai zuwa. Sa'an nan kuma, za a bai wa daga bangaren masu adawar mukanin firaministan sabuwar gwamnatin hadin gwiwa.

A ranar 11 ga wata, bayan da mista Bozize ya dawo birnin Bangui, hedkwatar Afirka ta Tsakiya, ya ce, yana sa ran cewa, bangaren masu adawa zai gabatar da sunan wanda zai zama firaministan kasar.

Tun tsakiyar watan Disambar bara ne kawancen 'yan adawa na Afirka ta Tsakiya wadda aka fi sani da suna SELEKA ya kaddamar da matakin soja, ya kuma mamaye wasu muhimman birane da garuruwan kasar cikin gajeren lokaci. A ran 11 ga wata, sassa daban daban na kasar ta Afirka ta Tsakiya masu gwagwarmaya da juna sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, inda kawancen SELEKA ya yi watsi da shirinsa na tube shugaba Bozize daga mukaninsa, don haka mista Bozize zai shugabanci sabuwar gwamnatin hadin gwiwa har zuwa lokacin da wa'adin mulkinsa zai cika a shekarar 2016. Har wa yau kuma, kawancen SELEKA ya yi nuni da cewa, a kwanaki da dama masu zuwa, zai tabbatar da ko an biya bukatunsa ta fuskar siyasa ko a'a.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China