Bisa kiran da kungiyar tattalin arzikin kasashen yankunan tsakiyar Afirka ECCAS ta yi, an yi taron kwamitin duba yadda ake tafiyar da "Yarjejeniyar samun zaman lafiya daga duk fannoni ta Libreville" a ran 9 ga wata a birnin Lebreville, inda wakilan gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya, kungiyar dakaru mai adawa da gwamnati ta Seleka, jam'iyyar adawa da gwamnati da kuma wakilan jama'ar kasar suka tattauna kan harkokin tsayar da rikice-rikicen da ake fuskanta a kasar, da kuma warware matsalolin da ake fama da su ta hanyoyin lumana, to amma ba a samu ci gaba ko kadan ba a yayin zaman shawarwarin.
Bisa matsayinsa na mai shiga tsakani, ministan harkokin wajen kasar Congo-Brazzaville kuma shugaban kwamitin Basile Ikoebe ya yi kokarin yin shawarwari a tsakaninsa da wakilan bangarori daban daban, amma zuwa yanzu babu wanda ya ja da baya ko kadan kan matsayarsa, shi ya sa, ya zuwa yanzu shawarwarin ya shiga halin kila-wa-kila. (Maryam)