Bisa labarin da kafar yada labaru ta kasar ta bayar an ce, ya zuwa yanzu, sojoji 1200 sun kama aikinsu yadda ya kamata, kuma sun fara yin sintiri a birnin Bangui hedkwar kasar ta Afrika ta tsakiya da ma sauran muhimman wurare. An ce, a ranar 5 ga wata sojojin Faransa ya mayar da martani ga masu dauke da makamai dake kokarin kai hari kan fararen hula da jami'an tsaro na Faransa a kusa da filin saukar jiragen sama dake Bangui.
Ministan tsaron kasar Faransa Jean Yves Le Drian ya sanar a ran 6 ga wata cewa, Faransa ta riga ta fara ayyukanta a Afrika ta tsakiya da za su shafe tsawon watanni shida, da zummar farfado da tsaron kasar, tare kuma da ba da taimako wajen jibge rundunar sojojin kasashen Afrika da dama. Wannan ya kasance matakin soja na biyu da Faransa take dauka a wannan shekara a Afrika. An ce, bisa rokon gwamnatin kasar Mali a watan Janairun shekarar bana, Faransa ta tura sojinta zuwa kasar ta Mali dake yammacin Afrika domin taimawa kasar dakile masu tsatsaurancin ra'ayi kishin islama dake arewacin kasar. Har ila yau, sojojin Faransa na cigaba da fafatawa a kasar Mali tare da masu fafutuka. (Amina)