in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faransa na fatan bangarori daban-daban na Afrika ta tsakiya za su yi shawarwari tun da wuri
2013-01-08 14:06:47 cri
A ranar 7 ga wata ne a gun wani taron manema labaru kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Faransa Philippe Lalliot ya nuna cewar, tun barkewar rikici a kasar Afrika ta tsakiya, Faransa ta sha yin kira ga bangarori daban-daban da abin ya shafa da su tsagaita bude wuta tare kuma da yin shawarwari cikin lumana, ba tare da wani jinkiri ba.

A kuma wannan rana, shugaban kasar Afrika ta tsakiya François Bozizé ya kai ziyara a kasar Kongo Brazzaville, inda ya bayyana cewa yana fatan kai ziyara a birnin Libreville hedkwatar kasar Gabon a ranar 8 ga wata kafin ya yi shawarwari da kungiyar adawa ta SELEKA.

Manufar ziyarar ita ce samun goyon baya daga shugaban kasar Kongo Brazzaville Denis sassou-nguesso wanda kasashe daban-daban na yankin tsakiyar Afrika suka sanya shi matsayin mai shiga tsakani a rikicin Afrika ta tsakiya.

Denis sassou-nguesso yana fatan warware rikicin kasar Afrika ta tsakiya ta hanyar yin shawarwarin zaman lafiya.

Dangane da batun ko François Bozizé zai ci gaba da mulkinsa ko kuma a'a, Denis sassou-nguesso ya ce wannan muhimmin batu ne da za'a  tattauna kansa yayin shawarwari da za a yi a birnin Libreville,  kuma a matsayinsa na mai shiga tsakani a rikicin na Afrika ta tsakiya, ba zai yi magana a madadin ko wane bangare ba. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China