Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya nuna damuwa sosai kan yadda dakaru masu adawa na Seleka ta kasar Afirka ta tsakiya suke kokarin shiga babban birnin kasar, wato Bangui ta hanyar amfani da matakan soja, kana ya yi kira ga dakarun da su dakatar da kai hare-hare, ya kuma jaddada cewa, bai kamata a warware rikicin kasar ta hanyar amfani da matakan soja ba.
Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su yi shawarwarin neman samun zaman lafiya a birnin Libreville dake kasar Gabon a mako mai zuwa. Kwamitin yana fatan bangarorin za su cimma daidaito kan wani shirin warware rikicin kasar don warware matsalolin dake kasancewa a kasar na dogon lokaci.
Hakazalika kuma kwamitin sulhun ya kalubalanci bangarorin da su amince da kai kayayyakin jin kai ga fararen hula na kasar Afirka ta tsakiya, da magance kai hare-hare ga fareren hula, da kuma girmama hakkin dan Adam. (Zainab)