Kakakin MDD Martin Nesirky ya fada yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a ko wace rana cewa, "tawagogin hadin gwiwar da MDD ta rura, sun ga yadda ake ta kwasar ganima da wawushe kauyukan da ke tsakanin Grimari da Bambari mai nisan kilomita 100, inda mazauna yankunan ke buya a cikin daji".
Ya ce wannan tawaga ita ce ta farko da aka tura shiyyar, tun tsakiyar watan Disamba, lokacin da gamayyar 'yan tawayen Seleka suka kwace manyan biranen da ke arewaci da tsakiyar kasar, ciki har da Bambari da Kaga Bandoro.
'Yan tawayen dai sun kwace kusan kashi 1 bisa 3 na kasar ne kafin yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanyawa hannu a ranar 11 ga watan Janairu a Libreville, babban birnin kasar Gabon.
Don haka, ya ce hukumar ta bukaci 'yan tawayen na Seleka da gwamnati, da su bari ma'aikatan agaji su kai dauki ga al'ummomin da ke bukatar taimako, a kasar da aka yi kiyasin mutane 80,000 rikici ya wargaza, baya ga karin 'yan gudun hijira 17,000 daga Sudan. (Ibrahim)