Sakamakon kokarin shiga-tsakanin da gamayyar tattalin arzikin kasashen yankin tsakiyar Afirka tayi, gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya da kawancen 'yan adawa wadda aka fi sani da suna SELEKA sun fara wata tattaunawa a ranar 9 ga wata a kasar Gabon. A rana ta uku cikin tattaunawar, bangarorin biyu suka cimma matsaya kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Bisa wannan yarjejeniya, an ce, bangarorin biyu sun amince da kafa gwamnatin hadin-gwiwa dake karkashin jagorancin Francois Bozize, kuma wa'adin aikinshi na mulki zai kare a shekara ta 2016. Haka kuma, za'a zabi daya daga cikin 'yan adawar kasar don ya zama firaministan gwamnatin hadin-gwiwa, kuma za'a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin a cikin shekara daya.
Yarjejeniyar ta kuma tanada cewa, gwamnatin hadaka zata dauki nauyin farfado da zaman lafiya da tsaro a kasar Afirka ta Tsakiya, da shirya zaben 'yan majalisar dokoki, tare kuma da sake tsara rundunar sojojin kasar. Bugu da kari kuma, dakarun dake waje da yankin gamayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka zasu janye daga kasar ta Afirka ta Tsakiya.
A nata bangaren, jami'ar dake kula da harkokin tsakiyar Afirka na Majalisar Dinkin Duniya madam Margaret Vogt ta bayyana cewa, za'a fara amfani da wannan yarjejeniya sa'o'i 72 bayan da aka sa hannu a kanta. A wani labarin kuma, an ce, za'a kafa gwamnatin hadin-gwiwa tun daga ranar 12 ga wata.
Bayan da aka cimma wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, mai magana da yawun kawancen SELEKA ya ce, yarjejeniyar da aka cimma, wani ci gaba ne da aka samu wajen farfado da zaman lafiya, amma a cikin nan da 'yan kwanaki masu zuwa, kungiyar 'yan adawa zata tabbatar da ganin cewa, ko za'a iya biyan bukatunta ta fuskar siyasa.
A wani ci gaba kuma, kwamitin sulhun MDD ya fitar da wata sanarwa a daren ranar 11 ga wata, inda ya yi maraba da matsayar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu masu gaba da juna a kasar Afirka ta Tsakiya, da kuma yin kira da su nuna sahihanci wajen aiwatar da yarjejeniyar, a wani kokari na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin dogon lokaci a wannan kasa.
Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin sulhun ya bukaci bangarori daban-daban da su bada tabbacin samar da agajin jin-kai ga mabukata ba tare da wani cikas ba kuma ba tare da wani jinkiri ba, da kuma sakin dukkanin fararen-hula da ake tsare da su nan take. Kwamitin sulhun ya bada kulawa matuka kan rahotannin da suka shafi keta hakkin dan Adam a rikicin kasar Afirka ta Tsakiya, da jaddada cewa, kamata yayi a dakatar da irin wannan aika-aika, da yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka aikata laifin.(Murtala)