Wani kudurin doka dake dauke da sa hannun shugaba Francois Bozize da fadar gwamnatin kasar ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana sunan Michel Dotodjia Am Nondroko dake matsayin shugaban kungiyar 'yan tawayen Seleka, a matsayin mataimakin firaminista, kuma ministan tsaron gwamnatin wucin gadin kasar.
Kafuwar wannan tsari na gwamnatin hadaka dai a kasar ta Afirka ta Tsakiya ya zo bayan shafe tsawon lokaci ana tattaunawa tsakanin gwamnatin da 'yan tawaye, inda daga karshe yarjejeniyar da aka cimma a Libreville ta tanadi kafa gwamnatin rikon kwarya da za a rika sabuntawa bayan shekara guda, yayin da kuma ake sa ran gudanar da zaben 'yan majalisar kasar a shekara mai zuwa.(Saminu)