A cikin jawabinsa, Mr Li ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin na samun bunkasuwa yadda ya kamata a halin yanzu. Sin ba ta dauki mataki na gajeren lokaci domin samun bunkasuwar tattalin arziki ba yayin da ta fuskanci koma bayan tattalin arizkin duniya da na gida, a maimakon kara gibin kasafin kudi da kara ba da rancen kudi, Sin ta dauki matakin daidaita harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni da tinkarar kalubaloli bisa ka'idar tabbatar da kiyasin da aka yi a gaba da sa kaimi ga karkata hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki.
Mr Li ya kara da cewa, sabon tunanin da aka dauka na daidaita harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni da wasu sabbin fasahohi za su taimaka wajen samun bunkasuwar tattalin arziki nan gaba. Bugu da kari, Sin za ta ba da tabbaci ga manufofin kudi, abin da zai samarwa kasuwannin duniya wani sako na tabbatar da kasafin da aka yi a gaba, kuma hakan ya zama muhimmin mataki da Sin ke dauka wajen sauke nauyin dake wuyarta na ba da gudunmawa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Amina)