in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin manyan jami'an kasar Sin da Birtaniya
2013-12-03 11:08:44 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da takwaransa na kasar Birtaniya David Cameron‎ a safiyar jiya 2 ga wata, a babban dakin taron jama'ar kasar Sin, ganawar da ta zamo ta farko da firaministocin kasashen biyu sun yi, tun bayan kafuwar sabuwar gwamantin kasar Sin.

Yayin ganawar tasu, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi, tare da cimma matsaya daya kan wasu manyan batutuwa na shiyya-shiyya da na kasa da kasa da ake ciki a halin yanzu.

Mr Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin da Birtaniya kasashe ne masu hangen nesa, suna kuma da tasiri sosai ga duniya, don haka bunkasa dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, manufa ce da ta dace da moriyar kasashen biyu, kuma za ta taimaka wajen samar da zaman lafiya, da wadata, da bunkasa duniya baki daya. Ya ce ya kamata, kasashen biyu su nacewa ka'idar mutunta juna, da samar da daidaito tsakaninsu, da fahimtar juna, tare da mai da hanakali ga cimma nasarar wasu manyan batutuwa da suke shafe su. Har ila yau Mr. Li ya bayyana fata na kasashen na yin aiki tare, domin samar da daidaito kan wasu manyan batutuwa cikin adalci, ta yadda za a ingiza dangantakar hadin kai tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni yadda ya kamata.

A nasa bangare, David Cameron cewa ya yi, gwamnatin kasar Birtaniya ta mai da muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai fatan kara yin mu'ammala bisa ka'idar amincewa da juna, da mutunta juna, da kuma zurfafa hadin kai tsakaninsu. Ya ce Birtaniya na mutunta ikon mulkin cikakken yankin kasar Sin, ta kuma amince cewa, yankin Tibet kashi ne kasar Sin, ba za ta kuma goyi bayan ware shi daga kasar Sin ba.

Ban da haka, Birtaniya na goyon bayan kafa wani tsarin ciniki na kasa da kasa mai budewa, tare da fatan kara hadin kai da kasar Sin a fannonin ciniki, da zuba jari, da sashen kimiyya da dai sauransu. Dadin dadawa, Birtaniya na fatan tuntubar kasar Sin kan wasu batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, tare da nuna goyon bayanta ga kungiyar EU, wajen habaka hadin kai da kasar Sin, da ingiza yunkurin kafa yankin ciniki cikin 'yanci tsakanin Sin da kasashen Turai. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China