in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya isa Bucharest, babban birnin kasar Romania
2013-11-25 19:32:59 cri

A yammacin ranar Litinin 25 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa Bucharest, babban birnin kasar Romania, domin fara ziyarar aiki a kasar a hukunce, tare da halartar taron shugabannin Sin da na kasashen tsakiya da gabashin Turai.

Takwaransa na Romania, Victor Ponta wanda ya tarbe shi a filin jirgin sama tare da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar, ya kuma shirya bikin maraba da zuwan tawagar gwamnatin Sin a karkashin jagorancin firaminista Li.

Bayan bikin, firaminista Li da takwaransa Ponta sun je fadar firaministan kasar Romania cikin mota daya domin yin tattaunawa a hukunce, wannan ne dai karo na farko da firaministan Sin ya kai ziyara a wannan kasar a tsakiya da gabashin nahiyar Turai cikin shekaru 19 . (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China