in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya halarci taron dandalin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai karo na uku
2013-11-28 16:19:42 cri
A ranar Talata 26 ga wata ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron dandalin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai karo na uku da aka yi a birnin Bucharest na kasar Romania, inda ya kuma ba da wani jawabi.

Mr. Li ya bayyana cewa, kasar Sin ta goyi bayan dunkulewar kasashen Turai, kuma hadin gwiwa da bunkasuwar kasashen Turai na da muhimmanci sosai ga bunkasuwar kasashen duniya, kuma ya dace da moriyar kasar Sin. Kana kasashen tsakiya da gabashin Turai wani muhimmin bangare na nahiyar Turai, sabo da haka, aikin karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen yadda ya kamata zai taimaka wa bangarori daban dadan wajen inganta hadin gwiwar dake bisa manyan tsare-tsare.

Ya kuma kara da cewa, kasashen tsakiya da gabashin Turai, kasashe ne dake samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, suna da makoma mai kyau. Kuma kasar Sin kasa ce mai tasowa, a halin yanzu, matsayin bunkasuwar bangarori biyu suna kama da juna, shi ya sa ya dace a karfafa hadin gwiwa wajen bunkasa dangantakar cinikayya da tattalin arziki dake tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai.

Mr. Li ya kuma bayyana shawarwari da dama don inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen bisa fannoni daban daban yadda ya kamata, da suka hada da, na daya, a ninka adadin cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai har sau biyu, na biyu, a kara samar da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a cikin hadin gwiwa, kana na uku, a kara ayyukan zuba jari tsakanin kamfanonin kasashen cikin himma da kwazo. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China