in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya fara ziyararsa karo na uku a wannan shekara
2013-11-25 09:59:59 cri

Firaministan kasar Sin Mr Li Keqiang ya tashi daga nan birnin Beijing a yau Litinin 25 ga wata, domin kai ziyarar aiki a kasar Romaniya, wanda ta kasance ziyara karo na uku ke nan da Mr Li ya yi a mukaminsa a wannan shekara, kuma karo na farko da wani babban jami'in kasar ya kai ziyara a kasashen waje bayan cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18.

Ziyararsa zuwa kasar ta Romaniya ta kasance karo na farko da firaministan kasar Sin ya kai a cikin shekaru 19 da suka gabata. Yayin ziyarar, ana sa ran Li Keqiang zai halarci ganawa tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai. Daga baya kuwa, Mr Li zai halarci taro karo na 12 na firaministocin mambobin kasashen kungiyar hadin kai ta birnin Shanghai SCO da za a yi a kasar Uzbekistan. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China