Firayin ministan kasar Sin Li Keqiang da ke halartar taron firayin ministocin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO karo na 12 a kasar Uzbekistan, ya gana da takwaransa na kasar Rasha Mista Dmitry Medvedev.
A lokacin ganawarsu, Mista Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin gyare-gyare a fannoni daban daban, da habaka bude kofa ga duniya, a kokarin raya tattalin arzikin kasar, da samun ci gaba a zaman al'umma,. Ya yi imani da cewa, yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin take yi za su bayar da sabuwar dama ga hadin kan Sin da Rasha.
Mr Li ya kara da cewa, kasar Sin tana son zurfafa hadin kai a fannonin makamashi, da zirga-zirga, da wutar lantarki da dai sauransu, da kuma habaka hadin kai a ayyukan more rayuwar al'umma bisa ga bukatun juna.
A don haka in ji shi, kasar Sin tana goyon bayan Rasha game da shirin wasannin Olympics a lokacin sanyi a Sochi da za ta yi, kuma Sin tana son yin kokari tare da Rasha don sa kaimi ga raya dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi.
Firaministan Li ya fadi cewa, kungiyar SCO ta kasance wani dandali mai muhimmanci da kasashen Sin da Rasha suke hada kansu bisa manyan tsare-tsare, don haka kamata ya yi bangarorin biyu su kiyaye mu'ammala a tsakaninsu, su yi kokari tare don raya kungiyar, ta yadda za su iya samun sabon kyakkyawan sakamako a fannonin tsaro da hadin kansu.
A nasa bangare, Mista Dmitry Medvedev ya yi nuni da cewa, Rasha tana son taimakawa juna tare da Sin, tana kuma son aiwatar da sakamkon da aka samu a taron ganawa na lokaci-lokaci tsakanin firayin ministocin Rasha da Sin da kuma ayyukan hadin kai da suka amince da su.
Rasha, in ji shi, tana son inganta hadin kai a tsakanin kasashen biyu a fannonin makamashi, da tattalin arziki da cinikayya, da zirga-zirga, da jigilar kaya da kuma hadin kai a tsakanin yankin Gabas mai nisa na Rasha da yankin da ke arewa maso gabashin kasar Sin., da zurfafa hadin kai a fannin tsaro, fahimtar juna bisa tsarin kungiyar SCO, don samar da zaman karko da albarka ga wannan shiyya. (Danladi)