A yayin shawarwarin, firaminista Li ya bayyana cewa, ya yi farin ciki da sake ganawa da mista Ponta bayan watanni hudu da suka wuce, wannan ya bayyana dangantaka ta musamman tsakanin Sin da Romania, kuma ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin kasashen biyu na bunkasa zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangare, firaminista Ponta ya ce, wannan ne karo na farko da firaministan kasar Sin ya kawo ziyara a kasar Romania bayan shekaru kusan 20 kuma hakan na da muhimmanci kwarai. Kasashen biyu za su yi shawarwari kan dangantaka a tsakaninsu, da hadin gwiwa, musamman ma a fannin tattalin arziki da cinikayya, tare da kokarin rattaba hannu kan wasu jerin yarjeniyoyin hadin gwiwa a wadannan fannoni.(Fatima)