in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labarai na ketare sun yaba shawarwarin da firaministan Sin ya gabatarwa kungiyar SCO
2013-11-30 20:54:07 cri

Kafofin watsa labaru da kwararru na ketare sun yaba da shawarwari shida, da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar, don gane da matakan da ya dace a dauka, wajen zurfafa hadin kai, da kyautata makomar kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO.

Da dama daga manazarta na ganin shawarwarin, za su haifar da karuwar hadin kai tsakanin mambobin kungiyar a fannoni daban daban, tare da samar da moriya ga gamayyar kasa da kasa a wannan shiyya.

Don gane da hakan wani kwararre daga cibiyar nazarin zamantakewar al'umma da siyasa ta kasar Rasha Dmitry Ontoev ya ce, mahalarta taron sun bayyana burinsu na kara hadin gwiwa a fannonin bankuna hada hadar kudi, don haka ake kyautata zaton cewa, kungiyar ta SCO za ta cimma burin ta don gane da hakan.

A nasu bangare kamfanonin dillancin labaru na 'Information Telegraphic Agency, da kafar yada labaru ta yanar gizo mai suna Ria Novosti dake Rasha, da kuma jaridar Narodnoye Slovo ta kasar Uzbekistan, da ma wasu karin kafofin yada labaru, fidda bayanai suka yi kan yadda wannan taro na kungiyar SCO karo na 12 ya gudana, tare da tsokaci kan abubuwan da Mista Li ya aiwatar yayin taron.

A ranar 29 ga watan nan ne dai Firaministan kasar ta Sin, ya halarci taron firaministocin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai a Tashkent, babban birnin kasar Uzbekistan, inda shugabannin da suka halarci taron suka yi musayar ra'ayoyi, don gane da sa kaimi ga batun hadin kan mambobin kungiyar a fannoni daban daban bisa tsarin kungiyar, da kara raya kungiyar da dai sauransu. Daga karshe wakilan sun cimma matsaya guda a fannoni da dama. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China