A yayin taron, ana sa ran firaminista Li zai bayyana manufar da Sin ke bi wajen inganta hakikanin hadin gwiwa da kungiyar ta SCO daga dukkan fannoni, kuma zai yi musayar ra'ayi da shugabannin kasashen kungiyar game da inganta hadin gwiwar kungiyar ta SCO da hanyoyin bunkasa ta, da sa kaimi ga samar da zaman lafiya da karko a wannan yanki.
Haka kuma, Mr. Li zai gana da shugaban kasar Uzbekstan Abduganiyevich Karimov, kuma zai yi shawarwari da takwaransa na kasar Shavkat Mirziyoyev, da sauran shugabannin kungiyar.
Firaministan kasar Sin ya isa kasar Uzbekstan ne bayan kammala shawarwari tsakanin shugabannin kasar Sin da na kasashen da ke yankunan tsakiya da gabashin Turai. (Bako)