in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya yi jawabi a gun taron firayin ministocin kungiyar SCO
2013-11-30 16:42:01 cri

Firaministan Sin Li Keqiang ya bayyana aniyar kasar Sin, ta ci gaba da kare abubuwan da aka gada na gargajiya, yayin da ake gudanar da sauye-sauye, da tsayawa kan doka, tare da habaka hanyoyin hadin kai, don tinkarar kalubalolin ci gaba.

Firaministan kasar ta Sin ya bayyana hakan ne yayin jawabi sa ga mahalarta taro na 12, na firaministocin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO da ya gudana a ranar 29 ga watan nan.

Mista Li Keqiang ya kuma kara da cewa kamata ya yi a aiwatar da ra'ayin da aka cimma yayin taron koli na Bishkek a watan Satumba bana, a kuma yi kokari tare, a kokarin wanzar da yanayin zaman lafiya da lumana, da cimma moriyar juna, da tsimin makamashi da samun bunkasuwa, da sa kaimi ga gaggauta raya wannan shiyya, ta yadda za a iya samar da moriya ga jama'ar kasashen dake karkashin wannan kungiya.

Bugu da kari, Mista Li ya gabatar da shawarwari guda shida, da suka hada da zurfafa hadin kai a aikin tsaro, da kara saurin hanyoyin sifiri, da sa kaimi da saukaka harkokin cinikayya da zuba jari, da hadin kai a fanning kudi, da kara azama kan hadin kai a fannonin kare hallitu da makamashi, da habaka hadin kai a fannin al'adu.

Ban da wannan, firaminista Li ya bayyana halin da Sin ke ciki dangane da raya kasa da yin gyare-gyare, yana mai cewa, tun daga watan Yuli wannan shekara kawo yanzu, kasar Sin na tafiyar da harkokin tattalin arzikin ta yadda ya kamata, ta kuma kara samun kyautatuwa.

Ya ce kasar Sin za ta iya cimma makasudinta a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, ciki hadda ma'aunin yawan karuwar tattalin arziki na GDP da zai kai kashi 7.5 bisa dari, tare da mizanin sarrafa hauhawar farashin kaya na CPI kasa da kashi 3.5 bisa dari.

Li ya ci gaba da cewa, Sin za ta ci gaba da yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki, don ganin kasuwa ta haifar da moriya mai muhimmanci, yayin da ake rarraba albarkatu, haka kuma Sin za ta tabbatar da samar da moriyar dake wuyan gwamnati, tare da kara bude kofa ga kasashen duniya.

Tuni dai Mista Li Keqiang ya dawo nan birnin Beijing a yau Asabar, bayan ya halarci ganawar da ke tsakanin shugabannin Sin da na kasashen da ke tsakiya da gabashin Turai, da kuma taron kungiyar hadin kai ta Shanghai karo na 12, da kuma ziyarar aiki da ya kai kasar Romaniya.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China