in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya aike da sakon taya murna ga taron tattaunawa tsakanin kasar Sin da kasashen Turai
2013-11-27 15:25:10 cri
A ranar 26 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya aike da sakon taya murna ga taron tattaunawa tsakanin kasar Sin da kasashen Turai karo na uku, wanda ke gudana a birnin Brussels.

A cikin sakon na sa firaminista Li ya bayyana cewa, yanzu haka kasar Sin da kungiyar EU suna kan wani muhimmin mataki na samun bunkasuwa. Ya ce a bana, tattalin arzikin Sin ya shallake kalubalen koma baya, kuma yana ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata. Haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa manufar yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje, a hannu guda kuma kungiyar EU ma, ta cimma burin kara mambobinta, kuma an bullo da halin habaka tattalin arzikin kasashen nahiyar ta Turai.

Li Keqiang ya yabawa taron tattaunawar, da kuma muhimmiyar rawa da taron ke takawa, wajen kara fahimtar juna tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, da inganta mu'amala, da shawarwari daga dukkan matakai, da sa kaimi ga yin hakikanin hadin gwiwa.

Mr. Li ya yi fatan kwararru, da masana za su ci gaba da ba da shawarwari, don kara ba da gudummawa wajen raya alakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai.

Shugaban hukumar kasashen Turai Herman Von Rompuy, wanda shi ma ya halarci taron, ya yi jawabin fatan alheri, yana mai cewa yunkurin karfafa gyare-gyare daga manyan fannoni da aka kaddamar a gun cikakken zaman taro na 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, zai haifar da babban tasiri, wajen kawo sabuwar dama ga raya dangantakar da ke tsakanin kasashen Turai da Sin. Rompuy yace kamata ya yi bangarorin biyu su inganta amincewa da juna, da yalwata hadin gwiwa, don ci gaba da inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen Turai da Sin, duka da nufin ba da gudummawa ga aikin samar da zaman lafiya, da lumana da kuma wadata a duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China