A ranar 25 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya rubuta wani bayanin mai taken "Gaisuwa daga wata nahiya mai nisa—sharhin da aka rubuta a gabannin shawarwari karo na 2 da ke tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen dake yankunan tsakiya da gabashin kasashen Turai".
Sharhin ya yi bayanin cewa, a shekaru sama da 60 da suka gabata, wato lokacin da aka kafa sabuwar kasar Sin, kasashen da ke yankunan tsakiya da gabashin kasashen Turai suka amince da kasar Sin a karon farko, abin da ya bude wani sabon babi wajen inganta hadin gwiwar sada zumunta a tsakaninsu. A cikin dogon lokaci, duk da bala'un da aka fuskanta daga indallahi ko matsalar tattalin arziki, kasar Sin da kasashen da ke tsakiya da gabashin Turai su kan taimakawa juna, kuma jama'ar bangarorin biyu ba za su manta da wannan dankon zumunci ba. A cikin karni na 21, wato a sabon yanayin da ake ciki, an samu sabon ci gaba kan dangantakar dake tsakaninsu.
Kasashen dake yankunan tsakiya da gabashin Turai sun zama muhimman mambobi cikin kasashen Turai. Kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen nuna goyon baya game da yunkurin dunkulewar kungiyar EU baki daya, kuma tana fatan ganin hadin gwiwar kasashen Turai ta samu wadata a nahiyar. Kasar Sin ta nuna goyon baya ga kasashen dake yankunan tsakiya da gabashin kasashen Turai su shiga kungiyar EU, kuma ta yi imani cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen da ke tsakiya da gabashin kasashen Turai daga duk fannoni ba ma kawai za ta amfanawa jama'ar bangarorin biyu ba, kana kuma za ta cusa sabbin abubuwa wajen raya alakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai cikin dogon lokaci.(Bako)