A cikin tsarin hadin gwiwar da aka fitar da shi a lokacin taron, shugabannin sun amince da ba da kwarin gwiwwa ga kanana da matsakaitan masana'antun kasashensu domin su taka muhimmiyar rawa a fagen tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu.
Bangarorin biyu sun kuma dauki aniyar inganta ciniki a fannin aikin noma, inda suka sanar da gudumuwarsu ta ganin an kafa kungiya ta hadin gwiwa da za ta inganta wannan bangare.
A ta fannin hadin gwiwar hada-hadar kudi kuwa, Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai sun sha alwashin habaka cudanya, ba da kwarin gwiwa ga hukumomin kudi domin su samu damar tafiyar da ayyukan hadin gwiwa a fannoni daban daban tare da amfani da kudin da aka ware na musamman har dalar Amurka biliyan 10 domin inganta ciniki da tattalin arziki a tsakaninsu.(Fatimah)