Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden a nan birnin Beijing.
Yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su kara yin hadin gwiwa, kuma yana fatan kasar Amurka za ta dauki matakan da suka dace na soke kayyadewar da ta yi game da fitar da kayayyakin fasahar zamani zuwa kasar Sin, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannin makamashi masu tsabta da dai sauransu. Kana kasashen biyu su yi kokarin kafa tsarin hadin gwiwar tattalin arziki dake bude kofa da yakini a yankin Asiya da tekun Pasific, tare da kara daidaita manufofin tattalin arziki na kasashen biyu don inganta hadin gwiwarsu da samun bunkasuwa tare.
A nasa bangare, Mr Biden ya bayyana cewa, kasar Amurka tana fatan ita da kasar Sin za su yi amfani da fifikonsu wajen kara yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, cinikayya, makamashi masu tsabta da dai sauransu, da kuma sa kaimi ga yin shawarwari kan kulla yarjejeniyar zuba jari a kasashen biyu. Kasar Amurka tana maraba da kamfanonin Sin da su kara zuba jari a kasar, kana za ta kara samar da kyakkyawan sharadi a fannin kasawanci. (Zainab)