in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin ruwan yakin kasar Sin ya fara aikin ba da tsaro ga jiragen ruwa masu dauke da makamai masu guba na kasar Sham
2014-01-08 16:52:51 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a ranar laraban nan 8 ga wata, cewa jirgin ruwan yakin kasar Sin mai taken "Yan Cheng" ya shiga sararin tekun kasar Sham a ran 7 ga wata, domin yin hadin kai da jiragen ruwan kasashen Rasha, Denmark da kuma Norway wajen aiwatar da aikin ba da tsaro ga jiragen ruwa dake jigilar da makamai masu guba.

Madam Hua ta nuna cewa, babban jami'in kawar da makamai masu guba, da babban magatakardar MDD dukkansu sun nuna gamsuwar su ga aikin da ake yi, inda suka bayyana cewa, wannan aiki ya kasance muhimmin mataki wajen kawar da makamai masu guba a kasar Sham.

Haka kuma, Madam Hua ta jaddada cewa jigilar da makamai masu guba na kasar Sham cikin sauri na da muhimmanci sosai ga aikin kawar da makaman a kasar, don haka kasar Sin ta yaba sosai ga kokarin da bangarorin da abin ya shafa suke yi.

Ban da haka, Madam Hua ta yi bayanin cewa kasar Sin za ta ci gaba da kokarin musayar ra'ayi da bangarorin daban-daban ta yadda za a gudanar da aikin ba da tsaro cikin lumana da daidaici. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v An tabbatar da lokacin gudanar da taron Geneva karo na biyu kan Sham 2014-01-07 11:15:32
v Jirgin ruwan soja na Sin ya kama hanyar tekun Bahar Rum 2014-01-02 20:39:40
v Kungiyar haramta makamai masu guba ta zartas da kudurin lalata makamai masu guba na kasar Sham a ketare 2013-12-19 16:40:57
v Magatakardar MDD ya nuna damuwa game da tabarbarewar al'amurra a rikicin Sham 2013-12-17 16:06:41
v Magatakardar MDD ya nuna damuwa game da tabarbarewar al'amurra a rikicin Sham 2013-12-17 11:03:17
v Amurka ta dakatar da ba da kwarya-kwaryar taimako ga 'yan tawayen arewacin kasar Sham 2013-12-12 16:18:51
v Sojin 'yantar da kasar Sham ba zai halarci taron Geneva ba 2013-11-27 17:17:37
v Ministan harkokin wajen kasar Sham ya jaddada wajibcin kawar da makamai masu guba 2013-11-27 15:59:40
v Tawagar gwamnatin kasasr Sham za ta kai ziyara a kasar Rasha 2013-11-18 15:45:29
v Kungiyar 'yan adawa da gwamnatin kasar Sham sun yarda da shiga taron Geneva bisa wasu sharudda 2013-11-13 11:00:24
v Rukunin adawa na Sham ya yarda zai halarci shawarwarin Geneva karo na biyu tare da wasu sharudda 2013-11-11 20:46:04
v Za a dakile ta'addanci, in ji firaministan kasar Sham 2013-11-05 14:57:11
v Ministocin kasashen Larabawa sun kalubalanci kungiyar adawa da gwamnatin kasar Sham da ta shiga taron Geneva karo na biyu 2013-11-04 16:31:58
v Yawan 'yan gudun hijira na kasar Sham da suka shiga Lebanon ya haura dubu 812 2013-11-04 10:35:10
v OPCW tace Sham ta cika alkawarinta na lalata masana'antun makamai masu guba 2013-10-31 20:20:59
v An yi ganawa tsakanin shugaban kasar Sham da wakilin musamman na MDD 2013-10-31 14:51:49
v Sin ta yi maraba da shirin kau da makamai masu guba na Sham 2013-10-28 20:33:29
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China