Babban jami'in hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ya ba da wani rahoto a ran 3 ga wata a Beirut babban birnin kasar Lebanon, inda ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, 'yan gudun hijira na kasar Sham da suka shiga kasar Lebanon ya kai fiye da dubu 812, wanda ya karu da dubu 12 bisa na makon da ya gabata.
Ban da haka, rahoton ya ce, dubu 725 daga cikin wadannan 'yan gudun hijira sun yi rajista a hukumar, sauran dubu 87 da suka jiran yin rajista kuma dukkansu na samun taimako mai kyau daga gwamnatin Lebanon da hukumomi da abin ya shafa na MDD.
Haka zalika, rahoton ya ce, hukumar na yin rajistar 'yan gudun hijirar kasar ta Sham ta hanyar tashoshin da ta kafa a wasu yankunan kasar Lebanon.
An ce, a watan Oktoba, yawan 'yan gudun hijira na kasar Sham da suka yi rajista ya kai dubu 52, wadanda aka tsugunar da su a arewaci da gabashin kasar ta Lebanon dake kusa da iyakar kasar Sham, da birnin Beirut, hedkwatar kasar da kuma kudancin kasar. (Amina)