in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin adawa na Sham ya yarda zai halarci shawarwarin Geneva karo na biyu tare da wasu sharudda
2013-11-11 20:46:04 cri

Babbar kungiyar adawa ta kasar Sham 'Syrian National Coaliton' ta bayar da wata sanarwa a ranar Litinin 11 ga wata cewa, kungiyar ta yarda zata halarci shawarwarin Geneva karo na biyu, amma sanarwar ta fayyace sharuddan da wajibi ne a biya bukatarta kafin yin shawarwarin.

Bisa labarin da muka samu daga kafar yada labarai ta BBC, an ce, kungiyar 'Syrian National Coaliton' ta yi kira a cikin sanarwar cewa, kafin shawarwarin Geneva, tilas ne a tabbatar da ganin hukumomin ceto sun samu iznin shiga cikin wuraren da sojojin gwamnati ke kewaye, da sake masu laifuffuka a fannin siyasa, kuma a mayar da samar da gwamnatin wucin gadi a matsayin makasudin shawarwarin Geneva.

Lallai wannan sanarwa ta zama karo na farko da kungiyar ta yi alkawarin shiga cikin shawarwarin Geneva.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sham ba ta mayar da martani ga sanarwar kungiyar 'Syrian National Coaliton' ba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China