in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba da shirin kau da makamai masu guba na Sham
2013-10-28 20:33:29 cri
Kasar Sin a litinin din nan 28 ga wata ta yi maraba da shirin gwamnatin kasar Sham na mika cikakken niyyar ta na lalata makamai masu guba ga kungiyar hana yaduwar makamai masu guba ta duniya,inji Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar,Hua Chunying.

A ganawar ta da manema labarai da ma'aikatar harkokin wajen Sin ta saba yi a duk rana,Madam Hua Chunying ta ce mika shirin da kasar Sham ta yi yana da babbar ma'ana ga samar da cigaba wajen warware matsalar makamai masu guba na kasar.

Ta ce kasar Sin tana goyon bayan kungiyar hana yaduwar makamai masu guba ta duniya wajen ganin an lalata tare da tantance makamai masu guba na kasar ta Sham.

A cewar kakakin,Kasar Sin za ta shiga aikin da zai kawo cigaba wajen ganin an tattauna yadda za'a yi a cimma wannan bukatar na kungiyar. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China