Sanarwar ta nuna cewa, babban sharadin dake sahun gaba shi ne, shugaba Bashar Al-Asaad ya yi murabas daga mukaminsa, kuma a haramtawa shugaban da magoyansa samun ko wace irin kujerar wakilci a gwamnatin wuci gadi, da ma gwamnatin da za a kafa a nan gaba.
Ban da haka, sanarwar ta nemi kasashen duniya da su samar da wata hanya a cikin kasar ta Sham, wadda za a yi amfani da ita wajen samar da kayayyakin jin kai, tare kuma da yin kira ga gwamnatin kasar da ta saki mutane da ake tsare da su bisa laifuffukan siyasa.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin Syria ta riga ta bayyana matsayinta na shiga taron, amma ta ki yarda da zama teburin shawarwari da wadanda ta kira 'yan ta'adda. Har ila yau gwamnatin ta ki amincewa da kasashen waje su sanya baki cikin tattaunawar da za a yi.
A hannu guda kuma, ragowar kungiyoyin adawar ba su cimma matsaya daya ba kan ko za su shiga taron ko kuwa a'a. (Amina)