Firaministan kasar ta Sham Wael al-Halki, ya sanar a jiya Litinin 4 ga wata cewa, lokaci kawai ake bukata wajen dakile ayyukan ta'addanci a fadin kasar.
Al-Halki ya kara da cewa, sojojin kasar na kokarin farautar 'yan ta'adda, tuni kuma suka maido da zaman karko da tsaro a wasu yankunan kasar.
Daga nan sai ya nanata cewa, kasar Sham za ta shiga taro karo na biyu da za a kira a birnin Geneva ba tare da gindaya wani sharadi ba. Ban da haka, a cewarsa, za a yi kuri'ar raba gardama domin tabbatar da shirin raya kasar a nan gaba.
A nasa bangare, yayin da ministan yada labaru na kasar Omran Zoabi yake zantawa da manema labaru a wannan rana, ya nuna cewa, taron da za a yi a Geneva zai kasance wani matakin siyasa, amma ba na mika mulkin kasa, ko kafa hukumomin wucin gadi ba. (Amina)