Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mr Qin Gang ya bayyana a yau Alhamis 2 ga wata a nan birnin Beijing cewa, jirgin ruwan kasar Sin mai aikin bayar da kariya ga jirgin ruwan da ke dauke da makamai masu guba na kasar Sham ya kama hanya a ran 31 ga watan Disamba na shekarar 2013, domin gudanar da aikinsa a tekun Bahar Rum.
Mr Qin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, wannan jirgin ruwa mai lakabi "Yan Cheng" ya ratsa mashigin Suez. Gwamnatin kasar Masar ta sassauta dokarta ta yadda jirgin zai samu saukin wucewa. Game da wannan mataki, Sin ta nuna yabowa sosai. An ce, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin za ta ci gaba da tuntubar bangarori daban-daban da wannan batu ya shafa domin ba da tabbaci ga aikin da jirgin yake yi. (Amina)