Mr. Ban wanda ya yi wannan kiran a cikin jawabinsa ga manema labarai na karshen wannan shekarar a cibiyar majalissar dake birnin New York na kasar Amurka, ya yi amfani da lokacin ya bayyana ayyukan da majalissar ta yi a cikin shekarar baki daya, tare da bayyana manyan kalubalen da za'a fuskanta a shekara mai zuwa.
Fiye da mutane 100,000 ne suka hallaka a rikicin kasar ta Sham, sannan majalaissar ta kiyasta cewa sama da mutane miliyan 6.3 sun rasa matsugunni tun lokacin da fada ya barke a watan Maris na shekarar 2011.
Babban magatakardar ya kuma bayyana cewa, yanzu haka fiye da mutane miliyan 2 'yan kasar suka tsere kasashen dake makwabtaka da su domin neman mafaka da suka hada da kasashen Jordan, Lebanon da Turkiya.
Ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba zai aika da gayyata na babban taron kasashen duniya a kan kasar ta Sham da aka kudurta za'a yi shi a ranar 22 ga watan Janairu mai zuwa a birnin Geneva karo na biyu da zummar tattauna hanyar kawo karshen wannan tashin hankali na sama da watanni 30.
Ya ce duk wanda aka gayyata domin wannan taro, dole ne ya ba da gudummuwarsa na ganin wannan taro an samu nasara, don haka ya yi kira ga mahukuntan kasar ta Sham da su kawo karshen wannan arangama domin a samu hanyar aikawa da kayyayakin jin kai. (Fatimah)