in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin shugaban kasar Sham da wakilin musamman na MDD
2013-10-31 14:51:49 cri

Shugaban kasar Sham Bashar Al-Asaad ya gana da wakilin musamman na MDD da AL kan rikicin kasar ta Sham Lakhdar Brahimi a jiya Laraba 30 ga wata a birnin Damascus, babban birnin kasar.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, ganawar tasu ta kasa da tsawon sa'a daya. Gidan telibijin kasar ya ruwaito shugaba Bashar Al-Asaad na cewa, ba za a cimma nasarar shawarwari ba, sai an daina goyon bayan 'yan ta'adda da kuma matsa lamba kan wadannan kasashe da suka baiwa 'yan ta'adda taimakon kudi da makamai da dai sauran ragowar hidimma.

Yini daya kafin a yi ganawar, Lakhdar Brahimi ya nuna cewa, akwai kuskure wurin labarin da wasu kafofin yada labaru suka bayar kan kiran da ya yi ga Bashar da ya shiga shawarwari ba bisa matsayin shugaba ba. Yana mai cewa, hakikanin abun da ya ke nufin shi ne, shawarwarin Geneva ya kasance wani taro ne tsakanin bangarori daban-daban da rikicin kasar Sham ya shafa, su ne za su zabi hanyar da kasar za ta bi nan gaba, ba wai shi ne ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China