A halin yanzu an riga an tabbatar da lokacin gudanar da taron Geneva karo na biyu kan rikicin Sham, a matsayin jagoran taron, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya gayyaci bangarorin da abin ya shafa su halarci taron.
A ran 6 ga wata Ban Ki-Moon ya bayar da wata sanarwa ta kakakinsa, inda aka bayyana cewa, za a gudanar da taron ne cikin wa'adi biyu, wato za a fara wa'adi na farko daga ranar 22 ga wata, bangarorin da abin ya shafa na duniya za su yi shawarwari bisa babban matsayi, inda za a yi taron shi ne birnin Montreux na kasar Switzerland, amma bisa shirin na da, ya kamta a yi taro a Geneva.
Shawarwarin da za a mai da hankali a kai a tsakanin bangarorin Sham za su gudana a cikin wa'adi na biyu, wato za a fara wannan aiki daga ranar 24 ga wata a fadar 'palace of nations' na birnin Geneva. Manzon musamman daga MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa game da Sham Lakhdar Brahim zai jagoranci wannan taro, wanda gwamnatin Sham da 'yan adawa za su tura wakilai a karon farko don yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakaninsu.
Wani jami'in MDD ya yi bayani kan dalilin da ya sa aka canza wurin yin taro wa'adi na farko daga Geneva zuwa Montreux, cewar Geneva akwai karancin otel-otel, kuma a Montreux ana iya tabbatar da tsaro da dai sauran bukatunsu. Sakataren harkokin waje ta kasar Amurka John Kerry da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov sun riga sun yi shirin zuwan Montreux don halartar taron.
Ban Ki-Moon ya sake nanata cewa, wannan taro dai zai zama wata muhimmiyar dama da za ta kawo karshen rikici a Sham, da maido da zaman lafiya, babban aiki na taron shi ne kafa wata gwamnatin wucin gadi da bangarori daban daban za su amince da ita a kasar Sham.(Danladi)