Ministocin kasashen Larabawa sun yi taro a jiya Lahadi 3 ga wata a birnin Alkahira idan cibiyar AL take, wanda ya samu halarar shugaban kungiyar adawa da gwamnatin kasar Sham mafi girma ta NCSROF Ahmed Jarba, domin tattauna kan batun kasar Sham cikin gaggawa, tare kuma da kalubalantar kungiyar adawa da gwamnatin kasar ta Sham da ta amsa kokarin da bangarori daban-daban da wannan batu ya shafa suka yi wajen kiran taron Geneva karo na biyu, ban da haka, sun neme ta tura wakilinta zuwa taron tun da wuri.
Sanarwar da aka bayar bayan taron, ta jaddada cewa, kasashen Larabawa sun goyi bayan NCSROF, ita kuma NCSROF ta nemi kasashen duniya da su ba da taimako yadda ya kamata wajen kiran taron Geneva na biyu da fitar da wani shirin warware rikicin kasar Sham cikin lumana. (Amina)