Salim Idris, shugaban babbar kungiyar adawa da gwamantin kasar Sham a cikin gida wato sojin 'yantar da kasar Sham ya bayyana a ran 26 ga wata cewa, sojin ba zai shiga taron Geneva ba, ban da haka, zai ci gaba da jan daga da sojin gwamnatin kasar har sai an sauke shugaba Bashar al-Assad daga mukamin sa.
Kafin wannan, babbar kungiyar adawa da gwamnatin kasar Sham a kasashen waje ta kawancen 'yan adawa da masu juyin juya hali ta taba amincewa da shiga taron na Geneva, amma da sharadi.
A ganin wassu manazarta, ko da idan bangarori daban-daban masu halartar taron Geneva sun cimma matsaya daya daga wasu fannoni kan batun kasar Sham, ba za a iya tabbatar da su ba saboda ganin rashin samun goyon baya daga masu dauke da makamai a kasar. (Amina)