Kwamitin zartaswa na kungiyar haramta makamai masu guba, ya shirya wani taro a ran 17 ga wata da dare, inda aka tattauna cikakken shiri da babban sakataren kungiyar Ahmet Ümzücü ya gabatar, dangane da lalata makamai masu guba na kasar Sham a ketare, haka zalika wani kuduri da aka zartas ya yi maraba da alkawarin da wasu kasashe ciki hadda kasar Sin suka yi, na bada tallafin kariya a teku yayin jigilar makaman.
Bisa wata sanarwar da kungiyar ta bayar a ranar 18 ga watan nan, an ce, makasudin shirin shi ne, kammala aikin lalata makamai masu guba na kasar Sham cikin lokaci, bisa ga jadawalin da aka tsara a baya.
A farkon wannan wata, kasashen Norway da Danmark sun sanar da daukar matakai cikin hadin gwiwa, don gane da jigilar makamai masu guba na kasar ta Sham ta hanyar ruwa zuwa ketare don lalata su. Haka nan kasar Sin da Rasha za su ba da hidimar kariya a kan teku ga wannan aiki.
Kungiyar haramta makamai masu gubar ta jaddada a cikin kudurin cewa, ta yi maraba ga goyon bayan da Sin da sauran kasashe suka ba ta.
Bisa jadawalin da aka tsara a baya, an ce ya kamata a lalata yawancin na'urori, da damarar makamai masu guba na Sham kafin ranar 31 ga watan Maris na shekara ta 2014, a kuma kammala aikin dukkan makamai masu guba kafin ranar 30 ga watan Yuni na shekara mai zuwa.(Danladi)