in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sham ya jaddada wajibcin kawar da makamai masu guba
2013-11-27 15:59:40 cri

Mataimakin firaminista kuma ministan harkokin wajen kasar Sham, Walid Muallem ya furta a ran 26 ga wata cewa, kasar Sham za ta cika alkawarinta na yin watsi da makamai masu guba, bisa bukatar da aka gabatar mata.

Bisa labarin da wata kafar yada labarun kasar ta Sham ta fitar, an ce Walid Muallem ya gana da Madam Sigrid Kaag, mai sulhuntawa na musamman na hadaddiyar kungiyar wakilai ta hukumar hana makamai masu guba da MDD, inda suka yi musayar ra'ayi kan hadin gwiwar da za a yi tsakanin kasar ta Sham da hukumar, da kuma MDD.

Yayin ganawar, Walid Muallem ya bayyana cewa, Sham za ta cika alkawarin da ta yi na kawar da makamai masu guba, da kauracewa hada aikin bincike da kuma kawar da makamai masu guba da siyasa, kuma za ta cika alkwarinta bisa lokacin da aka kayyade, da tabbatar da wannan aiki yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China