Tawagar gwamnatin kasar Sham za ta isa birnin Moscow na kasar Rasha a yau Litinin 18 ga wata, domin tattaunawa kan batutuwa dangane da taron Geneva karo na biyu da za a yi. Rasha ta tabbatar da zuwan tawagar, amma ba ta ba da tabbacin lokaci ba tukuna. Kakakin shugaban kasar Dmitry Peskov ya tabbatar da cewa, shugaban kasar Vładimir Putin ba zai yi shawarwari da tawagar ba.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, Rasha na kokarin sa kaimi ga kiran taron Geneva karo na biyu tun da wuri. A bangare daya, Rasha na ci gaba da yin mu'amala da mahukuntan kasar ta Sham, tare kuma da ba su taimako, da nuna goyon baya ga kokarin da kasar ke yi wajen yaki da ta'addanci. Sannan a wani bangare na daban, Rasha na kokarin tuntubar kungiyar adawa ta kasar.
Wasu masanan kasar Rasha sun lura da cewa, ko da yake, gwamnatocin kasashen biyu suna yin mu'amala sosai a tsakaninsu, kuma tawagar kasar Sham za ta kai ziyara a kasar Rasha, amma ba za a warware rikicin kasar Sham daga kokarin bangare daya kadai ba. (Amina)