Kungiyar Nijeriya da ake yi ma lakabin "juruma ta Afrika" ta taki sa'a domin tana cikin rukunin da babu kungiyoyi masu karfi da yawa baya ga Argentina wanda Nijeriya ta taba yin gasa tare da shi a cikin gasar cin kofin duniya a Afrika ta kudu, sannan kungiyar Bosnia ba ta taba halartar babbar gasar a baya ba, a nata bangaren kuma kungiyar Iran daga nahiyar Asiya ta samu koma baya sosai a shekarun baya-baya, abubuwan da da ake gani za su baiwa kungiyar Nijeriya damar cimma nasara a rukunin da take ciki.
Ban da haka, kungiyar Cote D'ivoire a karkashin jagorancin Drogba da kungiya daya kawai daga arewacin Afrika Aljeriya su ma suka sami sa'a. Cote D'ivoire ba za ta tinkarar 'yan takara masu karfi ba a cikin kungiya ta C, ganin Columbia, Greek, da Japan, ba su da karfi sosai idan an kwatanta su da Cote d'ivoire wadda ake mata lakabin babbar giwar Afirka. A bangare na daban, Aljeriya zai fuskanci Bulgium, Rasha da Korea ta kudu, wadanda su ma ba su da karfi sosai. (Amina)