A ranar 28 ga watan Afrilu na shekarar 1993, wani jirgin saman soja ya yi hadari a sakamakon lalacewar na'urorinsa, wanda ya fada cikin tekun Atlantika. Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 dake cikin jirgin, ciki har da 'yan wasan kwallon kafa ta kasar Zambia 18. A lokacin, kungiyar na wasan share fagen shiga gasar cin kwofin duniya ta shekarar 1994. A sabili da haka, wannan hadari ya haddasa mummunar hasara a tarihin wasan kwallon kafa na Zambia, har zuwa yanzu ba ta samu farfadowa ba.
A gun bikin tunawar, shugaban hukumar kwallon kafa na Zambia Bwalya Kalusha ya bayyana cewa, za a shirya wata gasar wasan kwallon kafa tsakanin 'yan wasan kasar da ta Zimbabwe, domin tunawa da 'yan wasan da suka mutu. Shi Bwalya ya kasance daya daga cikin 'yan wasan kungiyar Zambiya ta 1994,.wanda ya tsallake rijiya da baya sabo da bai shiga wancan jirgin sama ba. Sa'an nan wani jami'in ma'aikatar wasannin motsa jiki ta Zambia ya bayyana cewa, kungiyar kasar na kokarin shiga gasar cin kwofin duniya da za a yi a birnin Brazil a badi, hakan zai zama sadaukarwa ga wadanda suka mutu.
Bisa labarin da kafofin yada labaru suka bayar, an ce, iyalan wadanda suka mutu ba su samu kudin diyya daga gwamnatin kasar ba har zuwa shekarar 2002. Kawo yanzu dai, gwamnatin ba ta gabatar da cikakken rahoto dangane da wannan hadarin jirgin sama ba.(Fatima)