An yi wasan karshe ne dai a filin wasa na Mohammad Bin Zayed dake birnin Abu Dhabi na kasar hadaddiyar daulolin Larabawa, inda Nijeriya ta doke kasar Mexico wadda ke rike da kambin gasar a karon da ya gabata. Daukar kofin a karo na hudu da Nijeriya ta yi ya karya matsayin bajimtar da kungiyar kasar Brazil ta kafa, na zama zakara sau uku a gasar.
Dama dai, kafin wasan karshen, sai da kungiyar Sweden ta lashe ta Argentina da ci hudu da daya. Wanda hakan ya sanya Sweden din zama a matsayi na uku, yayin da kuma Argentina ta ke a matsayi na hudu. (Zainab)