A ranar Talata ne majalisar dattawan Najeriya, ta amince da wani kuduri, don karrama 'yan wasan Golden Eaglets da masu horas da su sakamakon nasarar da suka yi ta lashe kofin kwallon kafa na duniya na 'yan kasa da shekaru 17.
Majalisar ta amince da kudurin ne domin taya Najeriya murnar nasarar da 'yan wasan na Golden Eaglets suka yi a gasar, wadda aka gudanar a hadaddiyar daular kasashen Larabawa.
Shugaban kwamitin wasanni na majalisar dattawan Najeriya, Senata Adamu Gumba ne ya gabatar da kudurin wanda ya samu amincewar dukkan sanatocin.
Majalisar ta kuma taya 'yan wasan, masu horas da su da baki dayan 'yan Najeriya saboda kishi da hadin kan da suka nuna a lokacin gasar wadanda suka ba su nasarar lashe wannan kofi na karo na hudu. (Ibrahim)