Takardar sunayen 'yan wasan da kungiyar kwallon kafa ta kasar Kamaru (FECAFOOT) ta gabatar a ranar Litinin ta kunshi masu tsare raga biyu, masu kare gaban gidan mai tsaron raga shidda, 'yan wasan tsakiyar fili bakwai da masu neman zura kwallo raga guda biyar.
Yan wasa ne dake taka leda cikin kungiyoyin wasan zakara na kasar Kamaru, baya ga dan wasa Guy Roger Toindouba dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta "Esperance Sportive" ta birnin Tunis.
"Bayan karshen samun horo da kwarewa da zai fara daga ranar 12 zuwa 17 ga watan Janairu a birnin Yaounde, 'yan wasan Kamaru zasu buga gasar sada zumunci da kasar Burkina-Fsao a ranar Jumma'a, 13 ga watan Janairu" in ji mista Emmanuel Ndoumbe Bosso.
Sannan a ranar 17 ga watan Janairu, a Daoula babban birnin tattalin arzikin kasar Kamaru, 'yan wasan kasar zasu buga gasar sada zumunci ta biyu tare da 'yan wasan kwallon kafa na MENA na kasar Nijar.(Maman Ada)