A gasar zagayen farko ta yankin Afirka ta neman shiga gasar cin kofin duniya a wannan karo, kungiyar kasar Nijeriya, Malawi, Namibia da kuma Kenya suke cikin rukunin F. Bayan gasanni 5 a tsakaninsu, kungiyar kasar Nijeriya ta samu maki 9 da cimma nasarar gasa sau biyu da kuma yin kunnen doki sau uku. Yin kunnen doki a gasa ta karshe ya iya taimaki kungiyar Nijeriya wajen shiga zagaye na gaba.
Bayan da kungiyar Nijeriya ta samu nasara karawarta tare da kasar Malawi, ta samu maki 12 da kasancewa ta farko a rukuninta, da ba ta damar shiga zagaye na biyu.
Bisa jadawalin gasar, kungiyoyi 10 da suka zama matsayin farko a rukuninsu za su shiga gasar zagayen biyu a watan Nuwanba na bana domin fitar da kungiyoyi 5 da shiga gasar cin kofin duniya ta kasar Brazil a shekarar 2014. (Zainab)