in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana za ta gudanar da tsarin tushe na wasan kwallon kafa na hukumar FIFA
2012-04-20 15:29:57 cri
A ranar Alhamis da ta gabata, hukumar kwallon kafa ta kasar Ghana wato GFA, ta sanar da cewa, hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, ta zabi kasar Ghana a matsayin dandalin da za a gudanar da tsarin kwallon kafa na tushe na hukumar.

Wannan tsari da ke da burin tallafawa wajen bunkasa wasan kwallon kafa daga tushe, zai gudana daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Yuni na shekara ta 2012 a Kumasi, birnin kasar na biyu mafi girma ta fannin kasuwanci, da ke da nisan kilomita 278 daga arewacin Accra, babban birnin kasar.

A cikin wannan tsari, akwai halartar yara 'yan makarantu na Kumasi guda 100 masu shakaru daga 6 zuwa 12 , inda jami'i mai kula da kwarewa ta fannin bada horo a hukumar kwallon kafa ta kasar Ghana GFA, Francis Oti Akenten da jami'an hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za su bada horo.

Wannan tsari shi ne karo na farko da aka soma yi a kasar Ghana, tun da aka fara gudanar da shi a cikin wasu kasashen Afrika.

Tsarin tushe na hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA na kara bada muhimmanci ga kasar ta bangarori biyu, wato ba da ilmi da kuma motsa jiki ga yara maza da mata masu shekaru 6 zuwa 12 a cikin makarantu, al'ummomi da kuma kungiyoyi da aka girka.

Babban taken wannan tsari shi ne "gaba daya yawan mutane mu shiga wasan kwallon kafa yadda ya kamata." (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China