in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kwallon kafa ta Zimbabwe ta tsara sabon kundi
2011-11-04 10:50:00 cri
Hukumar kwallon kafa ta Zimbabwe ta kaddamar da wani kwamiti mai wakilai hudu na tsarin kundin ta don ganin sun fitar da wani sabon kundin da zai tafe daidai da tsarin hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA,a cewar gidan radiyon kasar alhamis din nan.

Sake tsara sabon kundin ya biyo bayan damuwa da ake dashi na yadda kundin ya kasa tafiya dai dai da dokar sashin wasannin motsa jiki da wassu ka'idoji na hukumar FIFA.

Lokacin da yake kaddamar da kwamitin a Harare, babban birnin kasar,Shugaban hukumar kwallon kafan na Zimbabwen Cuthbert Dube yace kundin da ake amfani dashi yanzu anyi hanzarin tsara shine a shekara ta 2009 don haka ya samu kuskuren wajen la'akari da cigaban wasanni kwallon kafa masu tasowa gaba.

A wani fanning kuma Hukumar kwallon kafan ta nuna damuwar ta game da yadda halin cin hanci da rashawa yayi kamari a tsakanin alkalan wassan kwallon kafanta na shiya shiya tana mai cewa hakan yasa masu son daukan nauyin wasannin na gudu a lokacin da ake matukar bukatar su,don haka Shugaban hukumar ya ce mai yuwuwa ne gasar kwallon kafa na Platinum-Dynamos alkalan kasar waje ne zasu sa ido.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China