Da yake shaidawa kamfanin dillacin labarai na Xinhua ta wayar tarho daga sakatariyar kungiyar kwallon kafa ta yankunan gabashi da tsakiyar Afrika (CECAFA) a Nairobi, Nicholas Musonye wanda shi ne sakataren kungiyar ya ce, an riga an tsara komai na gasar wanda ya hadar da hada kan dukkan mambobin kungiyoyi wajen neman samun babban kofi da kuma kyautar kudade a lokacin ..
Sakataren ya ce, mambobi kasashen da za su shiga gasar sun hada Kenya, Uganda, Rwanda, Eriteria, Habasha, Burundi, Somaliya, Sudan, tsibirin Zanzibar na kasar Tanzania, sai da wasu bakin kasashe biyu wanda za su yanke shawarar shigarsu a sati mai zuwa.
A shekarar bara, kungiyar CECAFA ta gayyaci kasar Kamaru da Cote d'Ivoire a matsayin masu baki, sannan daga bisani ita ma kasar Zambia ta shiga gasar bisa gayyata.(Salamatu).