in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Moussa Sow aka zaba zakaran "Ballon d'Or" na shekarar 2011 na kasar Senegal
2011-12-27 11:27:31 cri
Madakin kwallo kuma mai zura raga na kungiyar kwallon kafa ta Lille kuma fitacce a kasar Faransa, Moussa Sow aka zaba a ranar Litinin "Ballon d'Or" wato dan wasan kwallon zinari na kasar Senegal na shekarar 2011 a wani jin ra'ayi na jaridun wasannin motsa jiki na kasar Senegal a yayin wani zaben gorzon dan wasan shekara.

Moussa Sow ya kasance dan wasa mafi ta fuskar taka leda na wasan rukunin liga na farko tare da zura kwalaye 25 cikin raga. Haka kuma ya ci nasarar rubunya cikin kofi da wasan zakaru a cikin shakara guda tare da kungiyar Lille.

Baya ga haka kuma, Hortense Diedhiou, sarauniyar wasan jido an zabe ta a matsayin zakarar wasa ta Senegal.

Kuma jaridun wasannin motsa jiki sun zabi Stephane Badji gorzon dan wasan kwallon kafa na gida na shekarar 2011. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China